IQNA

Mayakan Ansarullah Sun Harba Makamai Kan Yankin Tsaro Na Al-faisal

23:49 - April 13, 2018
Lambar Labari: 3482565
Bangaren kasa da kasa, dakarun Yemen tare da mayakan Ansarullah sun harba makamai masu linzami kan yankin tsaro na Al-faisal da ke gundumar Jazan a Saudiyya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Aljazeera net cewa, a yau dakarun Yemen tare da mayakan Ansarullah sun harba makamai masu linzami kan yankin tsaro na Al-faisal da ke gundumar Jazan a Saudiyya a kudancin kasar.

Majiyoyin gwamnatin kasar ta Saudiyya sun tabbatar da wannan labar, amma sun ce an kakkabo makaman.

Dakarun Yemen dai sun yi alkawalin cewa a kowace rana za su harba makamai masu linzami a kan muhimman wurare na kasar Saudiyya a matsayin mayar da martani kan kisan kiyashin da Saudiyya ke kan al’ummar Yemen.

3705438

 

 

 

 

 

captcha