IQNA

Wata Mahardaciyar Kur’ani Daga Senegal Zata Halarci Gasar Auqaf

23:35 - April 15, 2018
Lambar Labari: 3482573
Bangaren kasa da kasa, Maimuna Lu wata mahardaiyar kur’ani mai tsarki daga kasar Senegal za ta halarci gasar kur’ani ta Auqaf da za a gudanar a Iran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya tsara sunayen mutane biyar da za su halari gasar kur’ani ta duniya da a za a gudanar a Iran daga kasar Senegal.

Bayanin ya ce dukkanin mutanen suna daga cikin fitattun makaranta da suka shahara wajen lamarin kur’ani mai tsarki, daga ciki kuwa har da mace guda.

Wannan shi ne karon farko da wata mace daga kasar Senegal za ta alarci wannan babbar gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da za a gudanar karo na talatin biya a kasar Iran.

Taron gasar dai zai fara ne daga karshen wannan mako, kuma zai ci gaba har tsawon kwanaki bakawai, a babban masallacin marigayi Imam Khomeni (RA) da ke birnin Tehran.

3705550

 

 

 

 

 

 

captcha