IQNA

An Sanar Da Wadda Za Ta Wakilci Tunisia A Gasar Kur'ani Ta Duniya A Iran

23:55 - April 16, 2018
Lambar Labari: 3482575
Bangaren kasa da kasa, Hadil Bin Jama'a makaranciyar kur'ani ta kasar Tunisia ita ce za ta wakilci kasar Tunisia a gasar kur'ani ta duniya a Iran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hadil Bin Jama'a yar shekaru 17 makaranciyar kur'ani ta kasar Tunisia ita ce za ta wakilci kasar Tunisia a gasar kur'ani ta duniya a Iran a bangaren mata, wanda shine karo na biyu da ake gudanar da gasar a bangaren mata.

Wannan gasar kur'ani ta duniya ana gudanar da ita ne a kowace shekara a Iran, kuma shi ne karo talatin da biyar da ake gudanar da ita a bangaren maza zalla, amma daga shekarar da ta gabata aka kara da bangaren mata.

A ranar Alhamis mai zuwa ce za a fara gudanar da gasar, tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya daban-daban, wadda za ta gudana a birnin Tehran.

3705960

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha