Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, sheikh Abdulaziz ma'alim Muhammad malami a garin nakuro na kasar Kenya ya yi kira zuwa ga hada kai tsakanin musulmi baki daya.
Malamin ya ce karfin musulmi na tattare da hadin kansu, kuma rarraba babu abin da za ta kawo musu illa rauni.
Haka nan kuma ya kara da cewa, idan musuli suka mike suka zama masu aiki da koyarwar addininsu, to za su zama abin buga misalia cikin dukkanin lamurra, da hakan ya hada har da ciyar da tatalin arzikin kasarsu gaba.