IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Rufe Mashigar Karem Abu Salim A Gaza

22:49 - July 11, 2018
Lambar Labari: 3482825
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta yi gargadi dangane da hadarin da ke tattare da rufe mashigar Karem Abu Salim a Gaza da Isra’ila ta yi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban zauren majalisar dinkin duniya, kakakin babban sakataren majalisar Farhan Haq ya bayyana cewa, akwai babban hadari dangane rufe mashigar Karem Abu Salim a Gaza da Isra’ila ta yi, wadda ita ce hanya da ake shigar da kayan masarufi a yankin.

Ya ce yanzu haka manzon musamman na majalisar dinkin duniya a Palastinu Meladinov ya fara tuntubar bangarorin Isra’ila da kuma Falastinawa kan wannan batu, da nufin samun damar sake bude wannan mashiga.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ce haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da rufe mashigar Karem Abu Salim, mashiga guda daya tilo da ake yin amfani da ita domin kai kayan masarufi ga al’ummar zirin Gaza.

3729093

 

 

 

 

captcha