Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wannan makon an fara wani shirin bayar da horo ga yara 60 na kan hardar kur’ani a lardin Jiza na Masar da nufin yin amfani da hotun bazara domin hardar kur’ani.
A bisa yadda aka tsara a kowace rana yaran za su hardace shafuka goma daga kur’ani mai tsarki.
A cikin watanni biyu da za a kwase ana gudanar da shirin yaran za su iya hardace surori masu yawa daga kur’ani, wasu ma za su iya hardace kur’anin ya danganta da kwazon yaro.