IQNA

UNICEF: Kusan Dukkanin Yara A Yemen Na Cikin Hadarin Yunwa

23:50 - October 08, 2018
Lambar Labari: 3483034
Bangaren kasa da kasa, hukumar tallafawa kananan yara ta majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, kananan yara a kasar Yemen suna cikin mawuyacin hali.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da UNICEF ta fitar, ta bayyana cewa kusan dukkanin kananan yara a kasar Yemen suna cikin hadarin mutuwa, sakamakon mummunan halin da suke ciki.

Bayanin na UNICEF ya kara da cewa, sakamakon hare-haren da jiragen yakin kawancen Saudiyya ke kaddamarwa a kan kasar ta Yemen, hakan ya yi sanadiyyar rushewar mafi yawan abubuwan da al’ummar kasar ke bukata domin rayuwa.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, a halin yanzu yunwa ita ce babbar barazana ga al’ummar kasar Yemen, musamman kananan yara, wadanda a halin yanzu suke mutuwa saboda rashin abinci, ga kuma kwalara saboda da sauran cututtuka masu hadari da suke lakume rayukan kananan yara.

3753951

 

 

captcha