IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Malamai Masu Fatawa Na Kasashen Musulmi A Masar

23:59 - October 16, 2018
Lambar Labari: 3483047
Bangaren kasa da kasa, an fara gudana da zaman taro na manyan malaman kasashen musulmi masu bayar da fatawa a kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun a jiya ne aka fara gudana da zaman taro na manyan malaman kasashen musulmi masu bayar da fatawa a kasar Masar karkashin kulawar cibiyar fatawa ta kasar Masar wato Dar Ifta.

Babbar manufar taron da ita ce samar da wani yanayi da tsari dangane da yadda malamai za su rika bayar da fatawa, da kuma kebance wasu sharudda na musamman na malamai masu fatawa, maimakon barin lamarin kowa ya yi abin da ya ga dama.

An bude taron ne da bayanin Shauki Allam babban mai bayar da fatawa na kasar Masar, da kumaMukhtar Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar.

Haka nan kuma taron yana samun halartar manyan malamai daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da na musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba.

3756405

 

 

 

 

 

captcha