IQNA

Kwamitin Tsaro Zai Gudanar da Zama Kan batun Kasar Yemen

23:35 - January 08, 2019
Lambar Labari: 3483296
Bangaren kasa da kasa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai gudanar da zama kan batun tattaunawar da bangarorin kasar Yemen suka gudanar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shafin yada labarai na Nashra ya habarta cewa, a gobe kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai gudanar da zama kan batun tattaunawar da bangarorin kasar Yemen suka gudanar a kwanakin baya a kasar Sweden.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani Martins Griffiths zai gabatar da rahoton da ya hada dangane ad zaman tattaunawar, da kuma ziyarar da ya kai a kasar ta Yemen tun bayan cimma yarjejeniyar.

Shi ma anasa bangaren babban mataimakin magatakardan majalisar dinkin duniya zai gabatar da nasa rahoton kan halin da ake cikia  kasar Yemen ta fuskar matsaloli da kuma taikamon da ake bukata domin magance wasu matsalolin kasar.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani Martins Griffiths ya bayayan cewa, akwai bukatar taimakon gaagwa, kuma hakan na bukatar a sake farfado da ayyukan tashar jiragen ruwa ta Hudaidah domin kai daukin gaggawa ga alummar kasar ta Yemen, musamman abinci da magunguna.

3779438

 

 

 

captcha