IQNA

An Gudanar da Zama Kan Take Hakkokin 'Yan Adam A Bahrain

22:48 - January 11, 2019
Lambar Labari: 3483306
Cibiyar kare hakkin bil adama da dimukradiyya a kasar Bahrain ta dauki nauyin shirya taron, tare da halartar wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama daga kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, Tashar talabijin ta luluatv ta bayar da rahoton cewa, ana gudanar taron ne a  birnin Beirut na kasar Lebanon, a daidai lokacin da aka cika shekaru 8 daidai da fara daukar matakai na soji da kisan gilla a kan 'yan kasa masyu neman a yi adalci da gaskiya a cikin sha'anin mulki a kasar Bahrain.

Tun a cikin shekara ta 2011 ce l'umar kasaer Bahrain suke yin kira ta hanyar lumana ga mahukuntan kasar, da su bayar da dama ga al'ummar kasar a damu su cikin sha;anin mulki da siyasa, kamar yadda kowane dan kasa yake da hakki a cikin lamarin kasar, maimakon mayar da kasa da al'ummarta da arzikinta da siyasarta duka mallakin sarki da iyalansa.

Inda al'umma suka bukaci sarki ya ci gaba da mulkinsa, amma a bayar ad dama ga jama'a su zabi 'yan majalisar dokoki da kansu, wadanda za su tsara kundina tsarin mulki da kuma zabne Firayi minister, wanda zai rika tafiyar da majalisar ministoci, buatar da masarautar kasar taki amincewa da ita, maimakon hakan ma sai kisa da kamu a kan duk wani mai irin wannan ra'ayi.

3780267

 

 

 

captcha