Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a jiya gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida a kasar Jordan ta yi kira da a dauki matakin ladabtar da tashar talabijin din da ta tozarta addini ta hanyar cin zarafin mahardata kur’ani mai tsarki.
A cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta bayan yin Allawadai da kakakusar murya, ta bayyana cewa addinin muslunci a wurin dukkanin musulmi yana gaba da komai, saboda haka ba abu ne da za a lamunta da shi ba wani bangare na watsa labarai yak eta hurumin muslunci a Jordan.
Daga karshe kungiyar ‘yan jaridun ta kasar Jordan ta yi da a dauki matakin bin kadun wannan lamari, domin hukunta dukkanin wadanda suke da hannu wajen watsa shirin da ya ci zarafin kur’ani.