IQNA

Ilhan Omar Da Rashida Tlaib Za Su karbi Visar Isra'ila

23:47 - July 21, 2019
Lambar Labari: 3483865
Bangaren kasa da kasa, jakadan Isra'ila a a Amurka ya ce za a bayar da visa ta ziyara ga Ilhan Omar da Rashida Tlaib.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Ran Darmaer jakadan Isra'ila a kasar Amurka ya bayyana cewa, za su bayar da izinin shiga Isra'ila da yankunan gabar yamma da kogin Jordan ga 'yan majalisar dokokin Amurka biyu.

Ya ce sakamakon irin kawance mai karfi da ke tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma girmama majalisar dokokin Amurka, ofsihin jakadancin Isra'ila ba zai iya hana wani dan majalisar Amurka shiga Isra'ila ba.

Frayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da batun bayar da izinin shiga ga wadannan 'yan majalisar Amurka biyu muuslmi.

Rashida Tlaib tana wakiltar jihar Michigan a majalisar dokokin kasar Amurka, yayin da Ilhan Omar take wakiltar jihar Minnesota a majalisar dokokin ta kasar Amurka.

Rashida Tlaib 'yar asalin Palestine ce, kuma mafi yawa daga cikin danginta suna rayuwa a yankunan gabar yamma da kogin Jordana  cikin Palestine, yayin Ilhan Omar kuma 'yar asalin Somalia ce, dukkansu sun shiga majalisar dokokin Amurka ne bayan lashe zaben 2018.

 

3828782

 

captcha