Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Paul Pogba dan kasar Faransa da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasar wasa da kuam man. United a Ingila, ya kawar da kwalbar giya ta Heineken daga gabansa a lokacin da zai gana da 'yan jarida a gasar Euro 2020 ranar Talata da ta gabata.
Wannan kuma ya biyo bayan irin wanann matakin ne da Cristiano Ronaldo ya dauka na janye kwalaben da ke dauke da Coca Cola daga gabansa tare da ajiye ruwa maimakonsu.
Da dama daga cikin musulmi dai suna kallon wannan matakin na Pogba a matsayin jarunta, kasantuwar musulmi wanda addinansa ya haramta shan giya ko ta'ammuli da ita.