IQNA

Wurare Masu Ban Sha'awa A Aljeriya Masu Shekaru Fiye Da 800 Na Ayyukan Addini Da Na Alqur'ani

20:23 - May 12, 2022
Lambar Labari: 3487284
Tehran (IQNA) Cibiyar addini ta Sidi Hassan Sharif ta kasar Aljeriya, wadda ta samo asali tun karni takwas da suka gabata, a yau ta kasance cibiyar gudanar da ayyukan addini da na kur'ani, da kuma daya daga cikin wuraren yawon bude ido na kasar.

A cewar Al-Shorouk cibiyar addini ta "Sidi Hassan Sharif" da ke lardin Satif na kasar Aljeriya na daya daga cikin tsofaffin gine-gine a kasar, wadda ta ke da shekaru sama da 800 a duniya, kuma tana nan a yau da tsarin gine-gine na musamman da ake ziyarta. 

Jaridar Al-Shorouq ta kasar Masar ta bayyana wannan cibiya cewa: Idan kuka ji sautin karatun kur'ani mai tsarki a tsaunukan garin Ain al-Ravi da ke arewacin lardin Latif, to ku sani cewa daga tsakiyar ginin cibiyar Sidi Hassan Al-Sharif ne. wanda ya kai fiye da karni takwas kuma ya zama fitila ga masana Har yanzu haka.

An kafa wannan cibiya a shekara ta 1203 miladiyya, daidai da shekara ta 624 bayan hijira, ta hannun Sidi Hassan Al-Sharif, daya daga cikin adalai na wancan lokacin, wanda ke da alaka da Imam Hassan Ibn Ali (AS).

Al-Eid Dali, mai kula da wannan cibiya yana cewa: “Wannan daya ne daga cikin wurare masu daraja na ambaton Allah da karatun ayoyinsa, wanda Hassan al-Sharif ma’abucin ilimi da nagarta ya gina shi, wanda ya kasance mai kawo gyara, malami kuma jagora a zamaninsa. kuma Allah Ya ba shi darajoji da ilimi."

مسجد سیدی حسن شریف جاذبه گردشگری و حوزه علمیه طلاب در الجزائر

مسجد سیدی حسن شریف جاذبه گردشگری و حوزه علمیه طلاب در الجزائر

مسجد سیدی حسن شریف جاذبه گردشگری و حوزه علمیه طلاب در الجزائر

مسجد سیدی حسن شریف جاذبه گردشگری و حوزه علمیه طلاب در الجزائر

4055423

 

 

captcha