Bangaren kasa da kasa; an fara gasar karatun kur'ani da hardada kuma Tajwidi gami da tafsirin kur'ani mai girma a ranar alhamis talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da gidan radiyon Kur'ani na Mauritaniya ya shirya a babban masallacin birnin Nuwakcit fadar mulkin kasar ta Mauritaniya.
2012 Apr 21 , 18:31
Bangaren harkokin Kur'ani : An kawo karshe da kammala gasar karatun kur'ani mai girma da harda musamman ga mata a garin Kazan fadar mulkin Tataristan kuma wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki ta samu kayatarwa da cimma nasara mai girma.
2012 Apr 16 , 14:25
Bangaren kasa da kasa;A ranar ashirin da shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a lardin Rasifiya na kasar Jodan aka rarraba kur'ani da aka rubuta ta hanyar sadarwa irin ta zama a cikin yaren kurmanci .
2012 Apr 15 , 17:32
Bangaren kasa da kasa: karkashin shirin raba kur'anai dmiliyan ashirin da biyar a kasar Jamus ga wadanda ba musulmi ba a wannan kasar tuni aka bada da raba kur'anai dubu dari uku kyauta ga mabukata a wannan kasa ta yammacin turai.
2012 Apr 14 , 17:34
Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka kawo karshen gasar karatun kur'ani mai girma gay an jami'a irakiyawa a birnin Karbala kuma Darul Kur'ani karim da ke karkashin hubbarin Imam Huseini (AS) a garin Karbala ya dauki dawainiya da hidimar gudanar da wannan gasa da bada horon karatun kur'ani ga yan jami'ar.
2012 Apr 10 , 17:36
Bangaren harkokin kur'ani mai girma: hukumar da ke kula da gidan radio da talbijin na jamhuriyar Tataristan ta shirya hanyar koyan karatun kur'ani da harda kuma ta bayyana cewa a shirye take ta fara watsa wag a dukan mai bukata a fadin kasar.
2012 Apr 05 , 17:22
Bangaren kasa da kasa: a ranar sha uku ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a birnin Maskat fadar mulkin wannan kasa aka fara gudanar da matakin karshe na gasar karatun kur'ani mai girma a wannan kasa ta Oman kuma wannan gasar karatun kur'ani mai girma ta hada har da hardar Kur'anin.
2012 Apr 03 , 15:52
Bangaren kasa da kasa: an haramta saye da kuma sayar da kur'ani mai girma bugon jamai'ar Azhar a fadin Palsdinu saboda yana kumshe da kurakure wajan bugashi .
2012 Apr 03 , 15:52
Bangaren ilimi da nazari: a ranar shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyta ne karamar jami'a ta koyar da kur'ani da ke yankin Gardan tawun na garin Lahur na kasar Pakistan ta fara koyar da karatun kur'ani mai girma a wani salon koyar da ilimin kur'ani na jeka da gidanka.
2012 Mar 28 , 15:40
Bangaren harkokin kur'ani mai girma: an shirya wata gasar karatun kur'ani mai girma da kuma hardarsa da aka yi a ranar shida ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da aka shiryawa yara kanana na Tatar a babban masallacin garin Najani Kamsak na jamhuriyar Tataristan.
2012 Mar 28 , 15:40
Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar kula da harkokin kur'ani a Jodan ta bayyana cewa; kasashe tara na duniya ne a halin yanzu suka bayyana cewa ashirye suke su turo wakilansu don halartar gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa karo na ashirin da za a yi a kasar ta Jodan.
2012 Mar 26 , 16:40
Bangaren kasa da kasa: a garin Sultan na kasar Jodan ne ak bude darul kur'ani na musamman ga mata kuma lokacin bude wannan cibiya ta kur'ani an samu halartar Aud Alfa'uri shugaban ofishin kula da harkokin addini a garin.
2012 Mar 26 , 16:40