IQNA

Sheikh Ibrahim Zakzaky Har Yanzu Yana Cikin Mawuyacin Hali

23:17 - August 12, 2016
Lambar Labari: 3480702
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar kare hakkokin ‘yan shi’a a duniya da ke da mazauni a kasar Amurka ta yi gargadi dangane da halin da Sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Nyn cewa, a jiya wata cibiyar kare hakkokin ‘yan shi’a a duniya da ke da mazauni a birnin Washington a kasar Amurka ta yi gargadi dangane da halin da Sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki a inda mahukuntan Najeriya suke tsare da shi.

Bayanin kungiyar yace an samu tabbataun bayani dangane da irin halin da sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki inda yanayin jikinsa yake kara muni, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, da kuma abin da kungiyar ta kira sakacin da ake yi da lafiyar tasa.

Haka nan kuma kungiyar ta kara da cewa, baya ga matsalar idanu da malamin ke fama da ita, da kuma hannunsa na hagu wanda shi ma yatsunsa basu yin aiki, jikinsa ma yana kara yin rauni matuka, wanda kumahakan yana tattare da hadari.

Akwanakin baya ne dai jami’an tsaron Najeriya suka ce suna tsare da sheikh Ibrahim Zakzaky domin tsaron lafiyarsa, kuma shi ne da kansa ya bukaci hakan, abin da iyalinsa da kuma makusantansa suka karyata.

Tun a cikin watan Disamban shekara ta 2015 ce dai aka kama sheikh Ibrahim Zakzaky tare da maidakinsa da kuma daruruwan mabiyansa, bayan da sojoji suka bude wuta a kan almajiransa da suka ce sun tsare hanya ga babban hafsan sojin kasar, sun hana shi wucewa.

Sakamakon tsare hanyar da sojoji suka ce an yi wa shugabansu, sun kashe daruruwan mabiy harka Islamiyya a Zaria, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta tabbatar da hakan, tare da rusa wasu gine-gine muhimmai mallakin harka Islamiyya, da hakan ya hada da gidan sheikh Zakzaky da kuma Husainiyar Bakiyatollah.

3522050

captcha