IQNA

Harkar Musulunci Za Ta Kalubalanci Hukuncin Gwamnatin Kaduna

22:12 - October 09, 2016
Lambar Labari: 3480838
Bangaren kasa da kasa, harkar muslunci za ta kalubalanci hukuncin da gwamnatin jahar kaduna ta yanke na haramta kungiyar ta hanyar doka.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, a ranar Juma’a da ta gabata ce gwanatin jahar Kaduna a tarayyar Najeriya ta sanar da haramta kungiyar ‘yan uwa musulmi a jahar wadda sheikh Ibrahim Zakzaky ke jagoranta.

Kakakin harkar musulunci Malam Ibrahim Musa ya bayyana cewa za su kalu balance wannan hukunci ta hanyar doka a kotu.

Gwamnatin jahar kaduna ta dauki wanan matakin ne dai a daidai lokacin da ake shirin gudana da tarukan Ashura na Imam Hussain (AS) wanda shi ne taro mafi girma da mabiya harkar musulunci suke gudanarwa a Zaria a kowace shekara.

Babban dalilin da gwamnatin ta bayar da shi ne mabiya harkar muslunci suna taka doka tare da tare hanyoyi a lokacin tarukansu, kamar yadda kuma tace ta yi hakan ne bayan da kwamitin bincike da ta kafa ya bukaci a haramta kungiyar.

Sai a nata bangaren harkar muslunci ta karyata dukkanin abubuwa da aka fada a matsayin hujja, tare da bayyana cewa akwai abin da shi kansa kwamitin ya abta wand aba a yi maganarsa ba, shi ne kisan mutane akalla 348 da aka bizne sua cikin rami guda a Kaduna, tare da yin kira da ahukunta sojoji da suka aikata hakan, amma gwamnatin Kaduna ba ta ambaci wannan ba.

Yanzu haka dai jagoran harkar musluncia Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky yana tsarea ahannun mahukunta ba tare da gurfanar da shia gaban kuliya ba, duk kuwa da cewa rahotanni sun tabbatar da cewa yanayin lafiyarsa na ci gaba da kara tabarbarewa, musamman ma idonsa guda da sojoji suka harba da bindiga wanda ya daina aiki, sai kuma gudan da ya rage yanzu ya fara samun matsala.

3536604

captcha