IQNA

Masu Bincike Kan Makamai Masu Guba Sun Isa Syria

23:46 - April 13, 2018
Lambar Labari: 3482564
Bangaren kasa da kasa, tawagar masu gudanar da bincike na hukumar hana yaduwar makamai masu guba sun isa Syria domin gudanar da bincike.

Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa, a yau tawagar masu gudanar da bincike na hukumar hana yaduwar makamai masu guba sun isa Syria domin gudanar da bincike a yankin Douma kan zargin yin amfani da sanadarai masu guba.

Wadannan jami’a dai za su fara ne da tattara duk duk wasu alamu kan yiwuwar yin amfani da makamai masu guba, domin gwada da su sanadaran da aka yi amfani da su yanin Khanshikhun, a ga ko sun yi daidai.

Bayan tattara bayanai da kuma shaidu da alamomi za a aike da su zuwa kasar Holland domin gudanar da bincike.

Aranar Asabar da ta gabata ce aka fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wasu suna kwance wasu kuma suna kakkafewa, inda kasashen turai suka dauki wannan a matsayin hujjar cewa an yi amfani da makamai masu guba kuma suka dora alhakin hakan kan gwamnatin Syria, yayin da Rasha ta bayyana hakan a matsayin wasan kwaikwayo na siyasa.

3705436

 

 

 

captcha