IQNA

Zakaran Barcelona Zai Gina Masallai A Mauritania

17:58 - July 19, 2018
Lambar Labari: 3482837
Bangaren kasa da kasa, Usman Domble dan wasan kasar Faransa da ke awasa Barcelona yana shirin gina masallaci a a yankinsu da ke Maurtaniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Usman Domble dan wasan kasar Faransa da ke awasa Barcelona wanda dan asalin kasar Mauritaniya ne yana shirin gina masallaci a a yankinsu.

Dan wasan ya bayyana hakan ne bayan kammala wasan cin kofin kwallon kafa na kasashen duniya ne a kasar Rasha wanda kasar ta Faransa ta dauki kofin.

Ya bayyana cewa babban abin arin ciki ne a gare shi ya gina masallaci a mahaifarsa da ke cikin kasar Mauritaniya.

An tafi da shi kasar Faransa ne tun yana karamin bayan da mahaifiyarsa ta yi hijira zuwa Faransa.

3731206

 

 

 

captcha