IQNA

Wani Mai Fafutuka A Morocco Ya Nemi A Cire Ayoyin Jihadi Daga cikin Kur’ani

23:48 - January 03, 2019
Lambar Labari: 3483278
Bangaren kasa da kasa, wani lauya mai fafutuka a kasar Morocco ya bukaci da a cire ayoyin jihadi daga cikin kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ahmad Asid lauya ne mai fafutuka a kasar Morocco, wanda yake ganin cire ayoyin jihadi daga cikin kur’ani mai tsarki shi ne hanyar magance matsalar ta’addanci da sunan addini.

Lauyan ya ce ayoyin jihadi a cikin kur’ani suna magana ne bisa wani yanayi wanda ya dangane wani lokaci wanda muuslmi suka samu kansu a ciki, wanda jihadin shi ne mafita a gare kuam aka saukar da shi, wanda yanzu lokacin ya sha banban a cewarsa, kuma wasu suna fakewa da hakan wajen aikata ta’addanci da bata sunan muslunci.

Sai dai wannan ra’ayi na Ahmad Asid ya fuskanci martani mai tsani daga jama’a musamman malaman addini a kasar ta Morocco, duk kuwa da cewa akwai wadanda suka goyi bayansa.

Ibrahim Bin Al-karrab daya ne daga cikin malaman addinin muslucnia  kasar Morocco da suke gabatar da wa’azi a fadin kasar, ya mayar da martani a kan wannan batu, inda ya bayyana cewa hakika akwai masu yin amfani da wasu ayoyin kur’ani da ke magana a kan jihadi wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci, amma wannan ba laifin kur’ani ba ne, jahilcinsu ne a kan kur’ani ya kaisu ga aikata hakan.

Ya ce ayoyin kur’ani tabbata ne ba a canja su ko cire su, domin haka Allah ya saukar da su, kuma duk wani yunkuri kan hakan yana a matsayin tozarta kur’ani.

3778180

 

captcha