Kamfanin dillacin labaran iqna, shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da MDD kan kisan fararen hular da Saudiyya ta yi a garin Saada, bayanin majalisar ya yi kakkausar suka kan wannan danyen aiki.
Lise Grande babbar jami’ar majalisar dinkin duniya a bangaren ayyukan agaji akasar emen ta bayyana cewa, hakika hare-haren da Saudiyya ta kaddamar a ranar Talata da ta gabata kan wata kasuwa a garin Sa’ada da ke arewacin Yemen aiki ne da ya cancanci tir da Allaawadai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, harin na Saudyya yay i sanadiyyar mutuwar fararen hula 14 da jikkatar wasu da dama daga ciki kuwa har da kananan yara.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama a duniya sun dora alhakin wannan kisan gilla a kan gwamnatin Amurka, sakamakon goyon bayan da take baiwa Saudiyya kan kisan farare hula a Yemen, da kuma sayar mata da makaman da ke kai hare-haren da su.