Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hulda da jama'a a hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, Rayadh Ni'amah Salman ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu cibiyoyi fiye da 10,000 ne suka yi rijistar sunayensu domin hidima a lokacin wadannan taruka masu albarka.
Ya ci gaba da cewa wadannan cibiyoyin za su gudanar da ayyuka na musamman a lokacin gudanar da tarukan arbaeen a Karbala, da hakan ya hada da taimaka ma marassa karfi, da kuma samar da wuraren hutawa akan hanyoyin isowa Karbala daga biranan da ake tasowa.
Haka nan kuma ya bayyana cewa dangane da lamurran tsaro jami'an tsaro sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan.
Abin tuni a nan dais hi ne, tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) na daga cikin tarukan da mabiya mazhabar shi'ar Alul bai ke gudanarwa tun fiye da shekaru dubu da suka gabata, duk da cewa a wasu lokuta ana samu canje-canje da kan jawo dakatar da tarukan a wasu lokutan.