IQNA

Babban Limamin Ghana Ya Bukaci Musulmi Su Yi Azumi Domin Neman Allah Ya Kawo Karshen Corona

23:49 - April 12, 2020
Lambar Labari: 3484706
Tehran (IQNA) babban limamin kasar Ghana ya bukaci musulmi su yi azumi domin rokon Allah ya kawo karshen cutar Corona.

Babban limamin kasar Ghana Sheikh Usman Nuhu Sharubutu ya kira musulmi da su yi azumi domin rokon Allah ya kawo karshen cutar Corona a duniya baki daya.

Malam Sharubutu ya bukaci da a yi azumin ne na kwanaki biyu, wato ranar Laraba mai zuwa da kuma ranar Alhamis.

Ya ce a kowane lokaci kofar addu’a a bude take, domin kuwa duk abin da ya karfin dan adam to maganinsa Allah ne kawai, kuma ta hanyar rokon Allah da yawaita addu’oi, da taimakon Allah za a samu hanyar kawo karshen cutar.

Bay ga haka kuma shehin malamin ya bukaci jama’a da su rika kiyaye dukkanin ka’idojin da jami’an kiwon lafiya suka saka domin kare kai daga kamuwa da wannan annoba.

Dag akarshe ya roki Allah da ya karshen wannan annoba ta corona a duniya baki daya.

 

3891102

 

 

 

 

 

 

captcha